Pular para o conteúdo
Publicidade

Oséias 4

Tuhuma a kan Isra’ila

1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,

gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo

a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.

"Babu aminci, babu ƙauna,

babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

2 Akwai la’ana ce kawai,4.2 Wato, a yi la’ana a kai yin ƙarya da kisa,

yin sata da zina;

sun wuce gona da iri,

kisankai a kan kisankai.

3 Saboda wannan ƙasar tana makoki,4.3 Ko kuwa ta bushe

kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace;

namun jeji da tsuntsayen sararin sama

da kuma kifin teku suna mutuwa.

4 "Amma kada wani mutum kawo tuhuma,

kada wani mutum zargi wani,

gama mutanenka suna kama da waɗanda

suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.

5 Kuna tuntuɓe dare da rana,

annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku.

Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,

6 mutanena suna hallaka saboda jahilci.

"Domin kun ƙi neman sani,

ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina;

domin kun ƙyale dokar Allahnku,

ni ma zan ƙyale ya’yanku.

7 Yawan ƙaruwar firistoci,

haka suke yawan zunubi a kaina;

sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.

8 Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena

suna kuma haɗamar muguntarsu.

9 Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke.

Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu

in kuma sāka musu saboda ayyukansu.

10 "Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;

za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba,

gama sun rabu da Ubangiji

don su ba da kansu 11 ga karuwanci,

ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,

waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.

12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace

suka kuwa sami amsa daga sanda.

Halin karuwanci yakan ɓad da su;

sun yi rashin aminci ga Allahnsu.

13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu

suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,

a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,

inda inuwa take da daɗi.

Saboda haka ya’yanku mata suka juya wa karuwanci

surukanku mata kuma suka shiga yin zina.

14 "Ba zan hukunta ya’yanku mata

sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba,

balle surukanku mata,

sa’ad da suka yi zina,

gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai

suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada,

mutane marasa ganewa za su lalace!

15 "Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila,

kada Yahuda ya yi laifi.

"Kada ku tafi Gilgal;

kada ku haura zuwa Bet-Awen.4.15 Bet-Awen yana nufin gidan mugunta (sunan Betel, wanda yake nufin gidan Allah).

Kuma kada ku rantse cewa, Muddin Ubangiji yana a raye!

16 Isra’ilawa masu taurinkai ne,

kamar karsana mai taurinkai.

Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu

kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?

17 Efraim ya haɗa kai da gumaka;

ku ƙyale shi kurum!

18 Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare,

sai suka ci gaba da karuwancinsu;

masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.

19 Guguwa za share su,

hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.

Veja também