Pular para o conteúdo
Publicidade

Cânticos 7

1 Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne,

Ya diyar sarki!

Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja,

aikin hannun gwanin sassaƙa.

2 Cibinki kamar kwaf ne

da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba.

Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama

wanda furen bi-rana ya kewaye.

3 Nonanki sun yi kamar bareyi biyu,

tagwayen barewa.

4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa.

Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon

kusa da ƙofar Bat Rabbim.

Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon

wadda take duban Damaskus.

5 Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel.

Gashinki ya yi kamar shunayya;

yakan ɗauke hankalin sarki.

6 Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi,

Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!

7 Tsayinki ya yi kamar itacen dabino,

kuma nonanki sun yi kamar ya’yan itace.

8 Na ce, "Zan hau itacen dabino;

zan kama ya’yansa."

Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa,

ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,

9 kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau.

Ƙaunatacciya

Bari ruwan inabi wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena,

yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.

10 Ni ta ƙaunataccena ce,

kuma sha’awarsa domina ne.

11 Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari,

bari mu kwana a ƙauye.

12 Bari mu tafi gonar inabi da sassafe

don mu ga ko kuringar ta yi ya’ya,

ko furanninsu sun buɗe,

ko rumman sun yi fure,

a can zan nuna maka ƙaunata.

13 Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu,

a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi,

sabo da tsoho,

da na ajiye dominka, ƙaunataccena.

Veja também