6 Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka,
kamar hatimi a hannunka;
gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa,
kishinta yana kamar muguntar kabari,
yana ƙuna kamar wuta mai ci,
kamar gagarumar wuta.8.6 Ko kuwa / kamar harshen wutar Ubangiji.
7 Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba,
koguna ba za su iya kwashe ta ba.
In wani zai bayar da
dukan dukiyar gidansa don ƙauna,
za a yi masa dariya ne kawai.
Ƙawaye