6 Sai na ce, "Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai."
7 Amma Ubangiji ya ce mini, "Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. 8 Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka," in ji Ubangiji.