Pular para o conteúdo
Publicidade

Irmiya 12

Damuwar Irmiya

1 Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji,

sa’ad da na kawo ƙara a gabanka.

Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka.

Me ya sa mugaye suke nasara?

Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?

2 Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa;

sun yi girma suna ba da ya’ya.

Kullum sunanka yana a bakinsu

amma kana nesa da zuciyarsu.

3 Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji;

kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai.

Ka ja su kamar tumakin da za a yanka!

Ka ware su don ranar yanka!

4 Har yaushe ƙasar za kasance busasshiya12.4 Ko kuwa ƙasar za tă yi makoki

ciyawar kowane fili ta bushe?

Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne,

dabbobi da tsuntsaye sun hallaka.

Ban da haka ma, mutane suna cewa,

"Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba."

Amsar Allah

5 "In ka yi tsere da mutane a ƙafa

suka kuma gajiyar da kai,

yaya za ka yi gasa da dawakai?

In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa,12.5 Ko kuwa In ka dogara a lafiyayyiyar ƙasa

ƙaƙa za ka yi a kurmin12.5 Ko kuwa a rigyawar Urdun?

6 Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka;

sun da kuka mai ƙarfi a kanka.

Kada ka amince da su,

ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.

7 "Zan yashe gidana,

in rabu da gādona;

Zan ba da wadda nake ƙauna

a hannuwan abokan gābanta.

8 Gādona ya zama mini

kamar zaki a kurmi.

Yana mini ruri;

saboda haka na ƙi shi.

9 Ashe, gādona bai zama mini

kamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin nama

da sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba?

Tafi ka tattaro dukan namun jeji;

ka kawo su su ci.

10 Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina

su tattake gonata;

za su mai da gonata mai kyau

kango marar amfani.

11 Za zama kango,

busasshiya da kuma kango a gabana;

ƙasar duka za zama kango

domin ba wanda ya kula.

12 A kan dukan tsaunukan nan na hamada

masu hallakarwa za su zo,

gama takobin Ubangiji zai ci

daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan;

ba wanda zai zauna lafiya.

13 Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa;

za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba.

Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe

saboda zafin fushin Ubangiji."

14 Ga abin da Ubangiji yana cewa, "Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu. 15 Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa. 16 In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, Muddin Ubangiji yana rayekamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata. 17 Amma duk al’ummar da ba saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta," in ji Ubangiji.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também