Pular para o conteúdo
Publicidade

Irmiya 47

Saƙo game da Filistiyawa

1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.

2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

"Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa;

za su zama kogi mai rigyawa.

Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta,

garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu.

Mutane za su yi kuka;

dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa

3 da jin motsin takawar kofatan dawakai,

da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba

da motsin ƙafafunsu.

Ubanni ba za su juye don su taimaki ya’yansu ba;

hannuwansu za su yi laƙwas.

4 Gama rana ta zo

da za a hallaka Filistiyawa

a kuma datse dukan waɗanda suka ragu

waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon.

Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa,

raguwa daga bakin tekun Kaftor.

5 Gaza za aske kanta cikin baƙin ciki;

Ashkelon zai yi shiru.

Ya raguwar da suke zama a fili,

har yaushe za ku tsattsage kanku?

6 "Za ku yi kuka kuna cewa, Wayyo, takobin Ubangiji

sai yaushe za ka huta?

Ka koma kubenka;

ka huta, ka yi shiru.

7 Amma ta yaya zai huta

sa’ad da Ubangiji ya umarta,

sa’ad da ya umarta shi

don faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?"

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também