A gidan mai ginin tukwane
1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. 2 "Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona." 3 Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen. 4 Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
5 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 6 "Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?" In ji Ubangiji. "Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.