11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. 14 Za ku same ni," in ji Ubangiji, "zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku," in ji Ubangiji, "zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta."
Publicidade