20 Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada 21 ya ce,
"Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,
tsirara kuma zan koma.
Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;
yabo ya tabbata ga Ubangiji."