Publicidade

Jó 28

12 Amma a ina ne za a iya samun hikima?

Ina fahimta take zama?

13 Mutum bai gane muhimmancinta ba,

ba a samunta a ƙasar masu rai.

14 Zurfi ya ce, "Ba ta wurina";

teku ya ce, "Ba ta wurina."

15 Ba irin zinariyar da za iya sayenta,

ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.

16 Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir,

ko sauran duwatsu masu daraja ba.

17 Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba,

ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.

18 Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya;

farashin hikima ya fi na lu’uluai.

19 Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba,

zallar zinariya ma ba isa ta saye ta ba.

20 "To, daga ina ke nan hikima ta fito?

Ina fahimta take zama?

21 An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai,

har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.

22 Hallaka da mutuwa suna cewa,

Jita-jitarta kaɗai muke ji.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-