Publicidade

Jeremias 31

31 "Lokaci yana zuwa," in ji Ubangiji,

"sa’ad da zan yi sabon alkawari

da gidan Isra’ila

da kuma gidan Yahuda.

32 Ba zai zama kamar alkawarin

da na yi da kakanni kakanninsu ba

sa’ad da na kama su da hannu

na bishe su daga Masar,

domin sun take alkawarina,

ko da yake na zama miji a gare su,"

in ji Ubangiji.

33 "Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila

bayan wannan lokaci," in ji Ubangiji.

"Zan sa dokata a tunaninsu

in kuma rubuta ta a zukatansu.

Zan zama Allahnsu,

za su kuma zama mutanena.

34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,

ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, Ka san Ubangiji,

domin duk za su san ni,

daga ƙaraminsu har zuwa babba,"

in ji Ubangiji.

"Gama zan gafarta muguntarsu

ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba."

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-