12 Yaya aka yi ka fāɗo daga sama
Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba!
An fyaɗa ka da ƙasa,
kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
13 Ka yi tunani a ranka ka ce,
"Zan hau zuwa sama;
zan ɗaga kursiyina
sama da taurarin Allah;
zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro,
a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.14.13 Ko kuwa arewa; Da Ibraniyanci Zafon
14 Zan haura can bisa gizagizai;
zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka."
15 Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari,
zuwa zurfafan rami.