Kaiton al’umma mai tayarwa
1 "Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,"
in ji Ubangiji,
"ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba,
suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba,
suna jibga zunubi a kan zunubi;
2 waɗanda suka gangara zuwa Masar
ba tare da sun nemi shawarata;
waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna,
don neman inuwar mafakar Masar.
3 Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya,
inuwar Masar za tă jawo muku kunya.
15 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,
"Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake,
cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku,
amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.