Publicidade

Isaías 35

Farin cikin waɗanda aka ceta

1 Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna;

jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo.

Kamar fure, 2 zai buɗu ya hudo;

zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki.

Za a maido wa Lebanon da darajarta,

darajar Karmel da Sharon;

za su ga ɗaukakar Ubangiji,

darajar Allahnmu.

3 Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi,

ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;

4 ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,

"Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;

Allahnku zai zo,

zai zo domin ya ɗau fansa;

da ramuwar Allah

zai zo don cece ku."

5 Sa’an nan idanun makafi za su buɗe

kunnuwan kurame kuma su ji.

6 Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa,

bebaye kuma su yi sowa don farin ciki.

Ruwa zai kwararo daga jeji

rafuffuka kuma a cikin hamada.

7 Yashi mai ƙuna zai zama tafki,

ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za cika da maɓulɓulan rafuffuka.

A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama,

ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.

8 Kuma babbar hanya za kasance a can;

za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki.

Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba;

za zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce;

mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.

9 Zaki ba zai kasance a can ba,

balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta;

ba za a same su a can ba.

Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,

10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo.

Za su shiga Sihiyona da rerawa;

matuƙar farin ciki zai mamaye su.

Murna da farin ciki za su sha kansu,

baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-04_23-13-58-