Pular para o conteúdo
Publicidade

Isaías 40

28 Ba ku sani ba?

Ba ku ji ba?

Ubangiji madawwamin Allah ne,

Mahaliccin iyakokin duniya.

Ba zai taɓa gaji ko kasala ba,

kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

za su sabunta ƙarfinsu.

Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

Veja também