29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.