1 "Ku zo, dukanku masu jin ƙishi,
ku zo wurin ruwaye;
ku kuma da ba ku da kuɗi,
ku zo, ku saya ku kuma ci!
Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara
ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
2 Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba,
ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba?
Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau,
ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.
3 Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni;
ku saurare ni, don ranku ya rayu.
Zan yi madawwamin alkawari da ku,
zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.
4 Duba, na mai da shi shaida ga mutane,
shugaba da kuma jagorar mutane.
5 Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba,
kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku,
saboda Ubangiji Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
gama ya darjanta ku."
6 Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;
ku yi kira gare shi tun yana kusa.