Ɗaukakar Sihiyona
1 "Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo,
ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.
2 Duba, duhu ya rufe duniya
duhu mai kauri kuma yana bisa mutane,
amma Ubangiji ya taso a kanki
ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.
3 Al’ummai za su zo wurin haskenki,
sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.