2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji
da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,
don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,
3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,
in maido musu rawani mai kyau
a maimako na toka,
man murna
a maimako na makoki,
da kuma rigar yabo
a maimako na ruhun fid da zuciya.
Za a ce da su itatuwan oak na adalci,
shukin Ubangiji
don bayyana darajarsa.