Hukunci da kuma bege
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
"Sama kursiyina ce,
duniya kuma matashin sawuna.
Ina gidan da za ku gina mini?
Ina wurin hutuna zai kasance?
2 Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,
ta haka suka kasance?"
In ji Ubangiji.
"Wannan mutum ne nake jin daɗi,
shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,
yana kuma rawar jiki ga maganata.