Pular para o conteúdo
Publicidade

Isaías 9

6 Gama a gare mu an haifa mana yaro,

a gare mu an ba da ɗa,

gwamnati za kasance a kafaɗarsa.

Za a ce da shi

Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki

Uban Madawwami, Sarkin Salama.

7 Game da girmar gwamnatinsa da salama

babu iyaka.

Zai gāji sarki Dawuda, yi mulki a matsayinsa,

zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,

tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.

Ubangiji Maɗaukaki ne

ya yi niyyar aikata wannan duka.Ubangiji

Veja também