Pular para o conteúdo
Publicidade

Isaías 58

3 Suna cewa, Don me muka yi azumi,

ba ka kuma gani ba?

Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu,

ba ka kuma lura da wannan ba?

"Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama

kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.

4 Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi,

kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe.

Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau

ku zaci za a ji muryarku can sama.

5 Irin azumin da na zaɓa ke nan,

rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa?

Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai

kuna kuma kwance a tsummoki da toka?

Abin da kuke kira azumi ke nan

rana yardajje ga Ubangiji?

6 "Irin azumin da na zaɓa shi ne,

a kunce sarƙoƙin rashin adalci

a kuma kunce igiyoyin karkiya,

a yantar da waɗanda ake zalunta

a kuma kakkarye kowace karkiya?

Veja também