Pular para o conteúdo
Publicidade

Isaías 6

9 Ya ce, "Je ka ka faɗa wa wannan mutane,

" Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;

Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.

10 Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;

kunnuwansu su kurunce,

idanunsu kuma su makance.

In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

su ji da kunnuwansu,

su fahimta da zuciyarsu,

su kuma juyo a kuma warkar da su."

Veja também