Publicidade

Isaías 61

Shekarar tagomashin Ubangiji

1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

domin Ubangiji ya shafe ni

domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

don in yi shelar yanci don ɗaurarru

in kuma kunce yan kurkuku daga duhu

2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,

don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

in maido musu rawani mai kyau

a maimako na toka,

man murna

a maimako na makoki,

da kuma rigar yabo

a maimako na ruhun fid da zuciya.

Za a ce da su itatuwan oak na adalci,

shukin Ubangiji

don bayyana darajarsa.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-