97 Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!
Ina tunani a kanta dukan yini.
98 Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana,
gama kullum suna tare da ni.
99 Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina,
gama ina tunani a kan farillanka.
100 Ina da ganewa fiye da dattawa,
gama ina biyayya da farillanka.