Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 139

13 Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

sa’ad da aka yi ni asirce.

Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;

dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

kafin ɗayansu kasance.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também