7 Ina zan tafi daga Ruhunka?
Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
8 In na haura zuwa sammai, kana a can;
in na yi gado a zurfafa, kana a can.
9 In na tashi a fikafikan safiya,
in na sauka a gefe mai nisa na teku,
10 can ma hannunka zai bishe ni,
hannunka na dama zai riƙe ni gam.