Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 141

Zabura ta Dawuda.

1 Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri.

Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.

2 Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa;

bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.

3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji;

ka yi tsaron ƙofar leɓunana.

4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu,

ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka

tare da mutane masu aikata mugunta;

kada ka bari in ci abincinsu.

5 Bari mutum mai adalci buge ni, alheri ne;

bar shi tsawata mini, mai ne a kaina.

Kaina ba zai ƙi shi ba,

duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.

6 Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse,

mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.

7 Za su ce, "Kamar yadda mutum kan yi huda tsage ƙasa,

haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari."

8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka;

a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.

9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini,

daga tarkon da mugaye suka sa.

10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu,

amma bari ni in zo in wuce lafiya.

Veja também