Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 142

Maskil ne142.0 Kan maganar, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce.

1 Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji;

na da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.

2 Na kawo gunagunina a gabansa;

a gabansa na faɗa wahalata.

3 Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina,

kai ne wanda ya san hanyata.

A hanyar da nake tafiya

mutane sun kafa mini tarko.

4 Duba ta damata ka gani;

babu wanda ya kula da ni.

Ba ni da mafaka;

babu wanda ya kula da raina.

5 Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

Na ce, "Kai ne mafakata,

rabona a ƙasar masu rai."

6 Ka saurari kukata,

gama ina cikin matsananciyar bukata;

ka cece ni daga waɗanda suke fafarata,

gama sun fi ni ƙarfi sosai.

7 Ka yantar da ni daga kurkuku,

don in yabi sunanka.

Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni

saboda alherinka gare ni.

Veja também