13 Mulkinka madawwamin mulki ne,
sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai.
Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa
mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
14 Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi
yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.