Publicidade

Salmos 150

1 Yabi Ubangiji.150.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 6.

Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;

yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;

yabe shi saboda mafificin girmansa.

3 Yabe shi da ƙarar kakaki,

yabe shi da garaya da molo,

4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,

yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

5 yabe shi da kuge mai ƙara,

yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

6 Bari kowane abu mai numfashi yabi Ubangiji.

Yabi Ubangiji.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-04_15-35-42-