3 Ko ka duba zuciyata,
ka kuma bincike ni da dare,
ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba;
na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
4 Game da ayyukan mutane kuwa,
ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina
daga hanyoyin tashin hankali.
5 Sawuna sun kama hanyoyinka
ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.