Pular para o conteúdo
Publicidade

Salmos 17

6 Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini;

ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.

7 Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki,

kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu

da hannunka na dama.

8 Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;

ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka

9 daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,

daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.

Veja também