1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;
ya juya wurina ya kuma ji kukata.
2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,
daga laka da taɓo;
ya sa ƙafafuna a kan dutse
ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,
waƙar yabo ga Allahna.
Da yawa za su gani su tsorata
su kuma dogara ga Ubangiji.
4 Mai albarka ne mutumin
da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,
wanda ba ya kula da masu girman kai,
waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
5 Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna,
abubuwan banmamakin da ka aikata.
Abubuwan da ka shirya mana.
Ba wanda zai iya faɗa maka su;
a ce zan yi magana in faɗe su,
za su wuce gaban misali a furta.
6 Hadaya da sadaka ba ka sha’awa,
amma kunnuwana ka huda;
hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.
7 Sa’an nan na ce, "Ga ni, na zo,
kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.
8 Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna;
dokar tana cikin zuciyata."
9 Na yi shelar adalcinka cikin babban taro;
ba na rufe leɓunana,
kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.
10 Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata;
ina maganar amincinka da cetonka.
Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka
a gaban taron jama’arka mai girma ba.
11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;
bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
12 Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni;
zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani.
Sun fi gashin kaina yawa,
har ma na fid da zuciya.
13 Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji;
Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.
14 Bari masu neman raina
su sha kunya su kuma rikice;
bari dukan waɗanda suke neman lalacewata
su koma baya da kunya.