Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 51

4 Kai kaɗai na yi wa zunubi

na yi abin da yake mugu a idonka,

ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana

aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

5 Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa

mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

6 Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;

ka koya mini hikima a wuri can ciki.

7 Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;

ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

8 Bari in ji farin ciki da murna;

bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

9 Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina

ka kuma shafe dukan kurakuraina.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também