Pular para o conteúdo
Publicidade

Salmos 51

7 Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;

ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

8 Bari in ji farin ciki da murna;

bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

9 Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina

ka kuma shafe dukan kurakuraina.

10 Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,

ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.

11 Kada ka fid da ni daga gabanka

ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.

12 Ka mayar mini farin cikin cetonka

ka kuma ba ni ruhun biyayya, riƙe ni.

Veja também