Pular para o conteúdo
Publicidade

Salmos 66

1 Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

2 Ku rera ɗaukaka ga sunansa;

ku sa yabonsa zama da ɗaukaka!

3 Ku ce wa Allah, "Ayyukanka da banmamaki suke!

Ikonka da girma yake

har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

4 Dukan duniya sun rusuna a gabanka

suna rera yabo gare ka,

suna rera yabo ga sunanka." Sela

Veja também