Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 78

1 Ya mutanena, ku ji koyarwata;

ku saurari kalmomin bakina.

2 Zan buɗe bakina da misalai,

zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan ,

3 abin da muka ji muka kuma sani,

abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.

4 Ba za mu ɓoye su wa ya’yanmu ba;

za mu faɗa wa tsara mai zuwa

ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,

ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também