1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;
tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
5 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.
7 Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai
ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.
8 Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;
ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.
9 Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;
ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.