Pular para o conteúdo
Publicidade

Salmos 119

9 Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?

Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.

10 Na neme ka da dukan zuciyata;

kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

11 Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata

don kada in yi maka zunubi.

12 Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji;

ka koya mini ƙa’idodinka.

13 Da leɓunana na ba da labarin

dukan dokokin da suka fito bakinka.

14 Na yi farin ciki da bin farillanka

yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.

15 Na yi tunani a kan farillanka

na kuma lura da hanyoyinka.

16 Na yi murna a cikin ƙa’idodinka;

ba zan ƙyale maganarka ba.

ג Gimel

Veja também