1 Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.
2 Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka.
Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.
3 Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
na kuwa kuɓuta daga abokan gābana.