1 Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala;
bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
2 Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki
yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
3 Bari yă tuna da dukan sadakokinka
yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela
4 Bari yă biya maka bukatan ranka
yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.