4 "Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata
da kuma yawan kwanakina;
bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.
5 Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai;
yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka.
Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum,
har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela
6 "Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa.
Yana ta yawo, amma a banza ne kawai;
yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.