Publicidade

Salmos 65

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa.

1 Yabo ya dace65.1 Ko kuwa kan jira; ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba. da kai, ya Allah, a Sihiyona;

a gare ka za mu cika alkawuranmu

2 Ya kai wanda yake jin addu’a

a gare ka dukan mutane za su zo.

3 Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu,

ka gafarta65.3 Ko kuwa ka yi kafara domin laifofinmu.

4 Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa

ka kawo kusa don su zauna a filayenka!

Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka,

na haikalinka mai tsarki.

5 Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci,

Ya Allah Mai Cetonmu,

begen dukan iyakar duniya

da kuma na tekuna masu nesa,

6 wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka,

bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,

7 wanda ya kwantar da rurin tekuna,

rurin raƙumansu,

da kuma tumbatsar al’ummai.

8 Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka;

inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe

kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.

9 Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa;

kana azurta ta a yalwace.

Rafuffukan Allah sun cika da ruwa

don su ba mutane hatsi,

don haka ne ka ƙaddara.65.9 Ko kuwa don haka ne ka shirya ƙasar

10 Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta;

ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.

11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka,

amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.

12 Makiyayan hamada sun cika har suna zuba;

tuddai sun rufu da murna.

13 Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna

kwari kuma sun cika da hatsi;

suna sowa don farin ciki.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-04_23-13-58-