3 Amma bari adalai su yi murna
su kuma yi farin ciki a gaban Allah;
bari su yi murna da farin ciki.
4 Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,
ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;68.4 Ko kuwa / ku shirya hanya wa shi da yake hawan ta hamada
sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.