Publicidade

Salmos 78

4 Ba za mu ɓoye su wa ya’yanmu ba;

za mu faɗa wa tsara mai zuwa

ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,

ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.

5 Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub

ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila,

wadda ya umarce kakanni-kakanninmu

su koya wa ya’yansu,

6 don tsara na biye su san su,

har da ya’yan da ba a riga an haifa ba,

su kuma su faɗa wa ya’yansu.

7 Ta haka za su dogara ga Allah

ba kuwa za su manta da ayyukansa ba

amma za su kiyaye umarnansa.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-