1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;
sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
2 Kowace rana tana yin jawabi;
kowane dare yana nuna sani.
3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta,
ba wani amon da aka ji daga gare su.
4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,
kalmominsu zuwa iyakokin duniya.
A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,
kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
6 Takan taso daga ƙarshen sammai
ta kewaye zuwa wancan;
babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce,
takan wartsakar da rai.
Farillan Ubangiji abin dogara ne,
suna mai da hikima da sauƙi.
8 Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,
suna ba da farin ciki ga zuciya.
Umarnan Ubangiji haske ne
suna ba da haske ga idanu.