4 Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
5 Gama a lokacin wahala,
zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;
zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa
ya kuma sa ni can a bisa dutse.